Posts

Tsibirin Shaidan Ko Tsibiri Bermuda Tsibiri Ne Da Labarinsa Ke Da Matukar Daukar Hankali

Image
Tsibirin Shaiɗan da ake wa laƙabi da "Bermuda Triangle" a Turance, tsibiri ne da  labarinsa ke matuƙar ɗaukar hankalin masu saurare. An sha bayyana labarinsa a cikin tatsuniyoyi da almara. A kodayaushe, akan bayyana abubuwan ban al'ajabi da ke faruwa a cikinsa. Daga cikin abubuwan al'ajabin da aka bayyana a wannan tsibiri na shaiɗan akwai wasu irin halittu da har yanzu ba a tantance ko waɗanne irin halittu ba ne. Sannan akwai Aljanu da dabbobi iri-iri. Wasu ma har sukan bayyana tsibirin da fadar shaiɗan. Wato a tasu fahimtar, karagar mulkin shaiɗan a nan take. A INA TSIBIRIN ALJANU YAKE? Masana da dama sun sha bayyana cewa tsibirin shaiɗan da ake wa laƙabi da "Bermuda Triangle" na nan a yammacin kogin Atlanta tsakanin  Florida, Puerto-Rico da Bermuda. A nan ne aka bayyana cewa wannnan fada ta Shaiɗan take. Ana yi masa laƙabi da fadar shaiɗan ne saboda al'ajabin da ke faruwa a cikinsa. Sai dai shahararren mai kuɗin nan kuma masanin kimiyya da fasaha na ƙa...